Babban taron hada kan marubuta da masu fasahar harshen Hausa na duniya baki daya.
Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya babban taro ne da ke tattara marubuta, manazarta, masu bincike, da masoya adabin Hausa daga sassan duniya daban-daban domin karfafa rubuce-rubuce, bunkasa harshe, da karrama kwarewar marubutan Hausa.